1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon hari ya kashe mutane a DR Congo

Abdul-raheem Hassan
September 6, 2021

Mambobin kungiyoyin farar hula sun zargi kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) mai alaka da kungiyar IS da kai harin a ranar Asabar a lardin Ituri da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/3zypN
DR Kongo Provinz Ituri | MONUSCO- Friedenstruppen
Hoto: Alexis Huguet/AFP

Wani jami'in yankin ya ce mutane 14 suka mutu a rahotannin farko bayan harin, amma ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa an gano karin gawarwaki a cikin daji kuma adadin na iya karuwa.

Sakamakon kazantar tashe-tashen hankula a kasar Kwango, wata rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Turai ta shiga tsakani a shekara ta 2003 karkashin jagorancin Faransa, amma bayan shekaru da dama na samun zaman lafiya, tashin hankali ya sake barkewa a shekarar 2017 inda aka kashe mutane akalla 50 a karshen watan Mayu 2021.