Denmak na shata shingen hana yaduwar cutar aladu | Labarai | DW | 29.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Denmak na shata shingen hana yaduwar cutar aladu

Hukumomin kasar Denmark na fargabar cutar muran aladun zai haifar da asarar sama da dala biliyan guda da ta ke samu a kasuwancin dabbobin zuwa kasashen waje.

Gwamnatin kasar Denmak ta ayyana fara aikin shata shinge mai tsawon kilomita 70 a iyakarta da Jamus in har cutar ba ta shiga Jamus ba, domin rigakafin yaduwar cutar muran aladu. Kasar Denmark na fitar da aladu akalla miliyan 28 a duk shekara, idan cutar aladun ya shiga kasar za a dakatar da hada hadar kasuwancin aladun zuwa kasashen da ke wajen Turai kuma hakan zai haifar da sarar sama da dala biliyan guda.

Sai dai matakin kariyar na shan suka daga 'yan majalisun Jamus, inda suke ganin cutar na yaduwa ne ta mutanen da ke safarar dabbobin da kuma wasu nau'ukan abinci.