De Maiziere na ziyara a yankin Magreb
February 29, 2016Ziyarar dai ta ministan harkokin cikin gidan Jamus din dai na zama wani yunkuri baya-bayan nan da hukumin Jamus su ke kan takaita kwarar 'yan gudun hijira zuwa kasar.
Ita dai wannan tattaunawar tsakanin kasashen biyu na zama yunkurin farko a cikin ziyarar kwanaki uku da Minstan yake a yankin Magrib da suka hada da kasashen Aljeriya da Tunisiya gami da ita kanta Moroccon don tattauna matsalar 'yan gudun hijira da kuma samun mafuta a tsakanin kasashen.
Thomas de Maiziere ya ce " a 'yan kwanakin nan masu neman mafaka daga Morocco da Algeriya da Tunisiya sun shigo Jamus da yawan su, wadanda ba su da damar zama a nan, a don haka akwai bukatarmu tattaunawa da gwamnatocin Morocco da Aljeriya da Tunisiya kan yadda za mu maido da su cikin nutsuwa, a shirye muke kuma mu tallafa wajen mai da su kasashen su na asali".