Daruruwa sun sake mutuwa a tekun Bahrum | Labarai | DW | 20.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daruruwa sun sake mutuwa a tekun Bahrum

Sama da bakin haure 700 ne rahotanni suka tabbatar da mutuwarsu bayan nitsewar da wani jirgin ruwa da ke fasakwaurinsu ya yi a tekun Bahrum.

Hatsarin wanda ya auku cikin daren Lahadin da ya gabata, lamari ne da aka bayyana shi da bala'i mafi muni da ya auku a tekun. Masu gadin tekun da ke aikin jigilar gawarwaki sun tabbatar da cewa ya zuwa safiyar wannan Litinin, mutane 28 kadai suka ceto da ransu cikin jirgin da ke shake da daruruwan mutanen da suka bar Libiya don tsallakawa nahiyar Turai.

Wani dan kasar Bangaladash, da aka kai asibiti da jirgi sama mai saukar Angulu, ya shaidawa wasu jami'an tsaro cewar mutanen da ke cikin jirgin da ya nitse fa, sun kai 950, wadanda suka hada da mata 200 da kuma kananan yara 50.

Ana dai sa ran zaman gaggawa yau Litinin, tsakanin shugabannin kasashen Turai kan wannan batu, kamar yadda kasar Italiya ta bukata, a dai-dai lokacin da kuwa kungiyoyi irinsu Amnesty International, ke cewa haduran na teku, hadura ne da ake iya kauce masu.