Dan kunar bakin wake ya hallaka mutane a Masallaci | Labarai | DW | 08.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dan kunar bakin wake ya hallaka mutane a Masallaci

Dan kunar bakin wake ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida a cikin babban masallacin Damboa da ke a jihar Bornon Najeriya.

Mutane shida sun mutu a wani sabon harin kunar bakin wake a wannan Jumma'a a garin Damboa dake jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya. Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriyar Kanal Sani Usman Kuka Sheka ya sheda wa kamfanin dillacin labaru na AFP cewa "Maharin ya tada bam din da ke jikinsa ne a cikin babban masallacin Jumma'a na Damboa, inda nan take ya hallaka kansa da wasu mutane shida da ke ibada a cikin masallacin."

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai a kan wadanda suka dau alhakin kai wannan hari, to amma a baya kungiyar Boko Haram ta sha daukar alhakin kai irin wadannan hare-hare da ke sanadiyyar rayukan al'umma a arewacin Najeriyar.