Babban kamu a satar 'yan Chibok a Najeriya
July 1, 2015Dakarun sojan Najeriya sun cafke wani dan kasuwa da ake zargi da hannu dumu-dumu a ayyukan 'yan Boko Haram na kwashe kusan yara dari uku 'yan makarantar nan ta Chibok a Arewa maso Gabashin Najeriya shekarar bara.
Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron kasar ta Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade ya ce Babuji Ya'ari jagora ne cikin ayyukan ta'addanci na masu ikirarin fafutikar addinin Islama amma yana bayyana kansa cikin ayyukan matasa 'yan kato da gora da ke ba wa al'umma kariya.
Wannan babban kamu dai na nuna yadda 'yan ta'addar suka shiga cikin 'yan kato da gorar da sunan aikin ba wa al'umma garkuwa, sannan wasu sojojin sun fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP wasu daga cikin mambobinsu suna zarginsu da zama mambobi na wannan kungiya ta Boko Haram mai asali daga Najeriya.
Da yake jawabi a daren jiya Talata Olukolade ya ce kamun wannan dan kasuwa ya sanya sun kai ga samun bayanai da suka kai su ga karin kamun wasu mata da ke aiki da wannan kungiya suna ba ta bayanai na sirri. Sai dai bai yi karin bayani ba kan mutane nawa ne aka kama ba koma yaushe aka kamasu.