Dage barazanar haraji kan motocin Jamus | Labarai | DW | 05.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dage barazanar haraji kan motocin Jamus

Bayan ganawa da Shugaba Trump,shugabannin kamfanonin kera motoci na kasar Jamus sun ce suna kyautata zaton Amirka ba za ta aiwatar da barazanar da ta yi ba ta dora haraji a kan motocinsu da ke shiga Amirka. 

Manyan daraktocin kamfanonin kera motocin na Jamus na Daimler da Dieter Zetsche da Volkswagen da Herbert Diess da BMW sun sanar da hakan ne bayan wata ganawa ta mintoci 30 da suka yi da Shugaba Donald Trump a jiya Talata. 

Ita ma dai daga nata bangare fadar White House a wani takaitacciyar sanarwar da ta fitar biyo bayan ganwar Shugaba Trump da shugabannin kamfanin kera motocin na kasar Jamus, ta ce Shugaba Trump ya bayyana fatan ganin kamfanonin kasar ta Jamus sun koma kera wani kaso na motocin nasu a kasar ta Amirka. 

A baya dai Shugaba Trump wanda ke zargin kasar Jamus da ci da gumin kasar ta Amirka a cikin huldar cinikayyar kasashen biyu ya yi barazanar dora harajin kaso 25 cikin dari kan motocin kasar Jamus da ake shigar da su a kasar ta Amirka.