Da tsakan daren wannan Alhamis sabon wa′adin da aka ba wa Girka ke cika | Labarai | DW | 09.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Da tsakan daren wannan Alhamis sabon wa'adin da aka ba wa Girka ke cika

An yi kira ga shugabannin kasar Girka da su gabatar da kwararan shawarwari game da matakan tsuke bakin aljihu.

Sa'o'i kalilan gabanin cikar wa'adi ga gwamnatin Girka ta gabatar da jerin sauye-sauyen tattalin arziki, kwamishinan lamuni na kungiyar Tarayyar Turai EU, Pierre Moscovic ya nemi gwamnatin birnin Athens ta gabatar da shawarwari masu gamsarwa.

Da tsakan daren wannan Alhamis wa'adin da aka ba wa Girkar da ta gabatar da sabbin shawarwarin yake cika. Idan ba ta cika wannan ka'ida ba to za ta fuskanci manyan matsaloli, inji kwamishinan lamunin na EU.

Bayanai daga kafafen kudi a birnin Athens sun ce sabbin matakan tsuke bakin aljihun za su shafi fannin yawon bude ido da soke 'yancin yin ritaya daga aiki gabanin wa'adi. Bankuna a Girka za su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa ranar Litinin.