Cutar Lassa ta kashe mutane 101 a Najeriya | Labarai | DW | 06.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar Lassa ta kashe mutane 101 a Najeriya

A cikin jihohin Najeriya 19 hadi da Abuja da ke bibiyar wannan cuta ta Lassa ce mutane suka kamu da kwayoyinta tare da rasa rayukansu.

Wasu bayanai da mahukuntan lafiya suka fitar a ranar Asabar din nan a Najeriya na cewa mutane 101 ne suka rasu sakamakon cutar Lassa a wannan kasa da ke a Yammacin Afirka.

Cibiyar da ke yaki da bazuwar cututtuka ta NCDC a Najeriyar ta ce rahotannin da ta samu sun nunar da cewa adadin wadanda suka kamu da cutar 175 ne cikinsu 101 sun rasu, tun bayan da aka fara bibiyar cutar a watan Agusta.

A cikin jihohin kasar dai ya zuwa yanzu 19 ne hadi da Abuja fadar gwamnatin kasar ke bibiyar wannan cuta wacce cikin wadanda suka rasu ta sanadinta har da na birnin na Abuja da Lagos da ma wasu jihohin 14 a cewar cibiyar ta NCDC.

Wannan kasa dai ta Najeriya nada yawan al'ummar da suka haure miliyan 170, abin da ke haifar da fargaba ta cewa ta yiwu ba a samun cikakkun bayanai na wadanda ke kamuwa ko suka rasu ta sanadin cutar ta Lassa mai nasaba da beraye.