Cutar hanta ta kashe mutane 25 a Diffa | Labarai | DW | 20.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar hanta ta kashe mutane 25 a Diffa

Wani sabon nau'in cutar hanta ta bullo a jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar, inda aka bada rahoton mutuwar mutane 25 yayin da 86 kuma suka kamu da cutar da Hepathitis E ko Hepatite E.

Kimanin mutane 25 sun rasa rayukansu a yankin Diffa da ke Kudu masu gabashin Jamhuriyar Nijar sakamakon kamuwa da wani sabon nau'in cutar hanta ta Hepathitis E ko Hepatite E a Faransance. Cikin wani bayani da ya yi wa manaima labarai a birnin Yamai, ministan kiwon lafiyar kasar Illiassou Mainassara ya nunar da cewar kimanin mutane 86 galibinsu mata masu juna biyu ne suka kamu da cutar ta hanta ya zuwa yanzu. Sai dai kuma ya tabbatar da cewa jami'an kiwon lafiya na daukar dawainiyar wadanda suka kamu da cutar da Hepathitis E ko Hepatite E a kyauta.

Daga cikin alamun kamuwa da cutar har da zazzabi da ciwon kai da amai da kuma ciwon ciki. Hukumomin lafiya na duniya sun nunar da cewar ana kamuwa da ita ta hanyar amfani da gurbataccen ruwa. Dama dai 'yan gudun hijira dubu 300 da aka tsugunar a yankin na Diffa na fama da rashin ruwan sha mai tsabta.  Dan majalisar dokokin Boulou Mamadou da ke wakiltar Diffa ya yi kira ga hukumomin Nijar da su gagauta kawo dauki ga wadanda suka kamu da cutar saboda suna cikin mawuyacin hali.