Ci gaba da rigakafin AstraZeneca a Jamus
March 19, 2021Talla
Matakin na zuwa ne bayan da hukumar tantance sahihancin magunguna ta Kunguyar Tarayyar Turai ta cimma mastaya kan tabbatar da ingancin rigakafin kamfanin AstraZeneca bayan gudanar da bicnike kan zargin illarsa a kan jama'a.
Yanzu haka dai kasashe da dama na duba yiwuwar ci gaba da amfani da allurar astraZeneka bayan samun tabbacin ingancinsa kwanaki kadan bayan da kaashen duniya da dama suka dakatar da amfani da allurar saboda zargin tana daskarar da jinin wadanda aka fara yi wa.