Chibok: Kwanaki 500 a hannun Boko Haram | Siyasa | DW | 27.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Chibok: Kwanaki 500 a hannun Boko Haram

‘Ya'yan kungiyar Boko Haram sun sace ‘yan matan makarantar sakandire ta garin Chibok su 276, har zuwa wannan lokaci ba’a kai ga ganosu ba ga kuma kungiyar Bring Back Our Girls na ci gaba da fafutika.

Symbolbild Nigeria Demonstration #bringbackourgirls Kampagne 500 Tage

'Yan fafutikar kwato 'yan mata da Boko Haram ke garkuwa da su

A talatainin daren 14 ga watan Aprilun 2014 ne dai aka yi awon gaba da ‘yan matan na garin Chibok a yanayi na ban mamaki fargaba da ma tababar faruwarsa ga mafi yawan al'ummar Najeriyar, domin shi ne irinsa na farko da ya taba faruwa.

Zuciyoyi sun dunguzuma tare da bakin ciki ya sanya hawaye a fuskokin iyayen ‘yan matan da ta kai wasu daga cikinsu rasa rayukansu saboda bakin ciki. Duk da gangamin da kungiyar Bring Back Our Girls da ta kwashe kwanaki 485 tana zaman dirshin a Abuja har zuwa wannan lokaci babu amo ko labarin inda ‘yan matan suke. Ga Malama Aisha Yesufu shugabar kwamitin tsara dubarun wannan gangami ta ce akwai dalilin da yasa suke ci gaba da jajircewa.

Buhari BBOGs

Shugaba Buhari lokacin ganawa da masu son ganin an kwato 'yan Chibok

"Fitowar da muke yi ya sanya duniya bata mance da ‘yan matan Chibok ba, domin ko ni in ba don kungiyar Bring back our girls ba da na mance da wannan batu. Lamarin da bakin ciki sosai amma dai har yanzu ,muna fitowa kuma zamu ci gaba da yin hakan muna kai kuka ga gwamnati har sai an samu ‘yan matan nan sun fito''

Irin yadda wannan gwagwarmaya ta samu dorewa har zuwa wannan lokaci duk da yunkurin shafa kashin kaji ga masu wannan fafutuka daga bangaren hukumomi a lokutan baya ya sanya Dr. Abubakar Umar Kari masani a kan hallayar bani adama cewa, ko da yake lamari ne na bacin rai amma ya shiga tarihi saboda ba'a taba ganin irinsa ba.

"Hakika wannan batu na ‘yan matan Chibok ya zama wani batu da ya zama ruwan dare game duniya, kuma dole a yabawa 'yan kungiyar Bring Back Our Girls duk da cewa kwalliya bata biya kudin sabulu ba, wannan wata gwagwarmaya ce wacce ba'a taba yin irinta ba a wannan kasa ko dai a wannan zamani".

Amma shin yaya ‘yan uwan yaran nan ke ji a yanzu da aka kwashe kwanaki 500 ba'a kai ga gano ‘yan matan ba? Mr: Hosea Tsambido Habana shi ne shugaban al'ummar Chibok da ke Abuja.

Nigeria Entführungen durch Boko Haram in Chibok

Al'ummar Chibok da Boko Haram ta sacewa yara.

"Gaskiya abin ya daure mana kai in ka yi magana cewa jin zafi a cikin zuciyarmu da jikinmu yafi nan. Kuma daga lokacin can makwanni biyu da sace ‘yan mata nan har yau babu wani labari da muka ji, amma da yake bamu ga gawarwakinsu ba to ba zamu fitar da rai ba''.

A yayin da ‘ya'yan kungiyar ta Bring Back Our Girls ta gudanar da zama na musamman a Alhamis din nan a Abuja don juyayin cika kwanaki 500 da gaza gano ‘yan matan na garin Chibok, an sake motsa zukata da ya kai ga zubda hawaye a wannan gwagwarmaya da ke ci gaba da daukan hankalin jama'ar Najeriya da na kasashen duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin