Chadi ta kawo dauki ga Nijar a yaki da BH | Labarai | DW | 08.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi ta kawo dauki ga Nijar a yaki da BH

Sojojin Chadi dubu biyu dauke da manyan makaman yaki sun kamo hanyar zuwa kasar Nijar domin taimaka wa sojojin kasar kwato birnin Bosso wanda ya fada a hannun mayakan Boko Haram

Rahotanni daga kasar Chadi na cewa sojojin kasar kimanin dubu biyu dauke da manyan makaman yaki sun kamo hanyar zuwa kasar Nijar domin taimaka wa sojojin kasar kwato birnin Bosso wanda ya fada a hannun mayakan Kungiyar a karshen makon da ya gabata inda Boko Haram din ta halaka sojojin Nijar 26 da na Najeriya guda biyu.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu rahotanni daga jamhuriyar ta Nijar ke cewa sojin kasar masu samun rakkiyar jiragen yakin kasar ta Nijar sun shiga yanzu haka farautar mayakan kungiyar ta Boko Haram a yankin na Bosso .

Sai dai za a iya cewa yanzu haka ana ci gaba da samun bayanai masu cin karo da juna a game da halin da ake ciki a yankin na Bosso inda majiyoyin ke cewa tuni garin na Bosso ya koma a hannun sojojin kasar ta Nijar wadanda suka yi nasarar fatatattakar mayakan kungiyar daga garin tun a washe garin harin na Jumma'a, a yayin da wasu rahotanni ke cewa sai a nan gaba ne sojojin kasashen biyu na Nijar da Chadin za su kaddamar da harin kwatar garin dama shiga farautar mayakan na Boko Haram a sansanoninsu.

Ko a shekara ta 2015 dai rundunar sojin kasar ta Chadi ta kai irin wannan dauki a kasashen Kamaru da Najeriya dama a Nijar a kokarin kasashen na murkushe kungiyar ta Boko Haram