Chadi ta kai Hari kan ′yan Boko Haram | Labarai | DW | 18.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi ta kai Hari kan 'yan Boko Haram

A wani mataki na mayar da murtani kan harin ta'addancin da aka kai a birnin Ndjamena, sojojin Chadi sun kai hare-hare ta sama a Tarayyar Najeriya kan maboyar 'yan Boko Haram.

A wata sanarwa da rundunar sojan kasar ta Chadi ta sanar a wannan Alhamis din, tace harin ya lalata a kalla sansani guda shidda na 'yan Boko Haram tare ta karkshe 'yan kungiyar da dama, kumata ce dakarunta na cikin shirin ko ta kwana, kuma zasu ci gaba da neman 'yan kungiyar Boko Haram a duk inda suka shiga, domin ta ce babu wani jinin dan Chadi ta za'a zubar ba tare da Chadi ta mayar da martani ba.

A hannu daya kuma hukumomin kasar ta Chadi sun saka dokar hana sanya Nikab jihabin nan da mata ke sanya wa da ke rufe ga baki dayan fuska kuma har kasa. A ranar Litinin ce dai da ta gaba wasu tawayen hare-hare suka yi sanadiyar rasuwar mutane 33 tare da jikkata wasu da dama a birnin na Ndjamena.