1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cece-kuce kan sarautar waka

Nasir Salisu Zango LMJ
December 18, 2025

Masoyan mawaki Dauda Kahutu Rarara na bayyana farin cikinsu da nadin da sarkin Daura ya yi masa, a matsayi sarkin wakar kasar Hausa. Amma kuma wasu kalaman da suka fito daga bakinsa, sun tayar da kura.

https://p.dw.com/p/55ci8
Najeriya | Katsina | Daura | Nadi | Sarki | Waka | Hausa
Wa ya dace da sarautar wakar kasar Hausa a Najeriya?Hoto: Faruq Azam/DW

Shekarar 2025 da muke bankwana da ita shekara ce da ta haskaka sarkin Daura bisa yadda yake ta nadin sarautu kamar saukar ruwan sama, cikin irin wadannan nade-nade ne aka nada Dauda Kahutu Rarara a sarautar Sarkin wakar kasar Hausa. Tuni dai galibin mutane musamman masoyan mawakin ke cewar ya cancanta, domin idan ana maganar waka da ake rerawa da harshen Hausa Rarara gwani ne.

Sabon sarkin wakar kasar Hausan Rarara ya bayyana cewar, daga yanzu duk me waka da Harshen Hausa sai ya yi mubaya'a gare shi. Sai dai wannan kira nasa ya bude shafin muhawara  a tsakanin mawaka, inda Adamu Hassan Nagudu ke cewa furucin na Rarara rashin sani ne domin sarautarsa iyakacin ta Daura.

Najeriya da Nijar: Fina-finan Hausa

Ban da Nagudu wanda shi ne sarkin wakar Borgu, shi ma sarkin wakar Sarkin Kano babban abokin hamayyar Rarara wato Naziru Sarkin waka ya ce, hakika sun gamsu an yi wa Rarara nadi amma fa kowa a garinsa Sarki ne. A cewarsa sarautarsa ba ta shafi kowa a cikinsu ba, tun da dai bikin magaji ba ya hana na magajiya.

To shin ko yaya masana ke kallon wannan furuci na Rarara? Farfesa Abdallah Uba Adamu masani ne da ke bincike kan harkokin al'adu da dangoginsu, ya ce sarauta irin wannan ba ta iko ba ce. Tuni dai Rarara ya ci gaba da yin shiga ta alfarma ta saraki, yana taku dai-dai a cikin fadarsa ana kuma yada hotunansa cikin wannan yanayi na kasaita.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani