1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Al'aduAsiya

Yankin Gulf na narka kudi a Hollywood don kare martaba

Mahmud Yaya Azare MAB
December 16, 2025

Zakewar da shugabannin kasashen Larabawan yankin Gulf suka yi wajen zuba makudan kudaden hannun jari a masana'antar shirya fina-finai ta Amurka da aka fi sani da Hollywood na ci gaba da jawo takaddama.

https://p.dw.com/p/55SE0
Birnin Los Angeles ya zama cibiyar raya masana'antar fina-finai ta Hollywood a Amurka
Birnin Los Angeles ya zama cibiyar raya masana'antar fina-finai ta Hollywood a AmurkaHoto: Barbara Munker/dpa/picture alliance

Kasashen Saudiya da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa sun zuba jari a kanfanonin Warner Bros da Telefax da Paramount da suka yi fice wajen shirya fina-finan a masana'antar Hollywood ta Amurka. Sai dai wadannan matakai na ci gaba da jawo cece-kuce a tsakanin 'yan yankin Gulf.

Karin bayani: Matakan inganta harkar hada fina-finan Hausa

A yayin da wasu ke danganta zuba jari a Hollywood da tsagwaron tsarin gasa a kasuwar jari hujja, sauran kuwa na danganta matakan da dalilai na cimma muradun siyasa ko dambaruwar al'adu.

Jarin dala biliyan 330 a harkar fina-finan 

Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani (Dama) yayin da yake marabtar Shugaban UAE Sheikh Mohamed bin Zayed Al-Nahyan
Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani (Dama) yayin da yake marabtar Shugaban UAE Sheikh Mohamed bin Zayed Al-Nahyan Hoto: Qatar Amiri Diwan/newscom/picture alliance

Imran Bin Talal, daya daga cikin masu kanfanonin zuba jari na Saudiya Aresco, ya ce dalilan neman samun riba ne ta sanya kasashen yankin Gulf shiga wannan sabuwar hanyar hada-hadar kudin ta zamani. 

Ya ce: "Kasashen Saudiya da Daular Larabawa da Qatar sun zuba kimanin dala biliyan 330 a harkokin shirya fina-finan da ake amfani da su a kafofin sadarwa na zamani. Yin hakan na daya daga cikin dabarun sabonta hanyoyin samun kudaden shiga ga kasashen daga ketare."

Kasashen da ke da arzikin man fetur sun yi ammanar cewa zuba jari a Hollywood na daya "daga cikin manyan hanyoyin da za su iya samar da makudan biliyoyin daloli ba daga man fetur da suke da shi ba” in ji Imran Bin Talal.

Cece-kuce kan manufar zuba jari a Hollywood

Wasu kungiyoyin kare hakkin bil'Adama da masu fafutukar kare al'adun yammacin duniya na korafin cewar, ba wa wadannan kasashen damar yin babakere a harkokin fina-finai na iya sanya kangi a kirkire-kirkre marasa iyaka da kanfanonin suka yi fice a kansa, lamarin da zai kai ga jefa su cikin duhun jahiliya.

Karin bayani: Dharmendra: Babban bango ya fadi a Bollywood

Kanfanonin Netflix da Warner-Bros na aiki tare a fannin shiryawa da yada fina-finai
Kanfanonin Netflix da Warner-Bros na aiki tare a fannin shiryawa da yada fina-finaiHoto: Dado Ruvic/REUTERS

A hannu guda kuma, masana ilimin halayyar bil'Adama, irin su Dr Sa'ad Junaid na ganin cewar akwai tarin dalilai na siyasa da ke sanya sarakunan da shugabanni na Larabawa zuba makudan kudadensu a abin da a kasashen gabashin duniya da na Musulmai ke dauka a matsayin sharholiya.

Ya ce kasashen na kokarin farautar tsuntsaye biyu da dutse daya ne a batun zuba jari a kanfanonin shirya fina-finai na duniya: "Zuba irin wadannan kudaden da suka wuce hankali a hada-hadar shirya fina-finai ba a banza ake yi ba. Da fari, kasashen na son daga martabarsu a idon duniya da wanke su daga tuhume-tuhumen ayyukan ta'addanci da galibin tsofin fina-finan Hollywood ke dangantawa Larabawa, sai kuma batun tuhumarsu da ake da mulkin kama karya da bautar da mata da danne hakkin tsiraru da 'yan bokon da ke hankoran sauyi a kasashensu.Sai kuma uwa uba, su no son a dinga shirya fina-finan da za su kara shagaltar da al'ummominsu."

Shagaltar da al'umma ko neman riba ?

Mohammed bin Salman na Saudiyya ya yi wa Donald Trump alkawarin kara zuba jari a Amurka
Mohammed bin Salman na Saudiyya ya yi wa Donald Trump alkawarin kara zuba jari a AmurkaHoto: Mark Wilson/abaca/picture alliance

A Takaice dai, shugabannin yankin Gulf na son al'umma su shagaltu ga barin neman sauyi ko kallon yadda wadannan masarautu ke cin karensu babu babbaka. Dr Muneef Ashraf, wani marubuci a kasar Saudiya ya ce da walakin kan zarge-zargen da ake yi wa kasashen na Gulf kan zuba jarin da suke yi.

Ya ce: "Ni a ganina, idan har aka ce an zuba jari don gyara sunan kasa ko jawo mata farin jinni, wannan ba laifi ba ne. Batun kuma ace ana kokarin wofantar da hankulan 'yan kasa ta hanyar fina-finai, wannan tamkar raina hankalinsu ne. Su ne ya kamata su fahimci haka, su fada da bakinsu, ba wasu 'yan bani na iya ba."