Matakan inganta harkar hada fina-finan Hausa | Zamantakewa | DW | 14.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matakan inganta harkar hada fina-finan Hausa

Gwamnatin jihar Kano a Najeriya, ta shirya wa masu fina-finai bita ta musamman, ta yadda fina-finan da suke shiryawa za su dace da bukatun al’uma.

Hiphop Nigeria (youtube.com/Jimana Hamzarto)

Wasu matasan arewacin Najeriya

A karon farko, gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta shirya wa masu fina-finan Hausa bita ta musamman, ta yadda fina-finan da suke shiryawa za su dace da bukatun al’uma; da kuma yin gyara ga irin kura-kuran da ake samu. Matasa masu fina-finan a wannan masana’anta na fannoni daban-daban ne gwamnatin Kanon ke baiwa horon domin sun kaiga shirya fina-finai masu ma’ana da za su karbu ga jama’a.

Haussa Schauspieler, Shehu Hassan Kano (privat)

Wani taurarun fina-finan Hausa

An dai jima ana jan hankalin masu shirya fina-finan Hausa a Najeriya dangane da fitowa da wasu abubuwan da bas a dacewa da bukatun al’uma masu kallo, wanda ginshiki ne babba da ya sa ake gudanar da horon. Shigowar gwamnati da nufin yin gyara ga irin kura-kuran da masu fina-finan ke yi, zai kawo ci gaba da ake so.

 

Baya ma ga batun kura-kurai, akwai kuma batun rashin kayan aiki na zamani da ke shafar ingancin harkar ta fina-finan Hausa a Najeriya. Mahalarta bitar dai, sun bayyana farin ciki da abubuwan da suka amfana da su a fannonin duka, da suka hada da gyaran kura-kuran da kuma karuwar. Horon, ya hada ne da batun nakaltar yin fim a rubuce da kuma na fita don gabatar da shi a aikace da zimmar samar da gajerun fina-finan na gwaji, domin auna fahimtar kowane daya daga cikinsu.