Jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta samu gagarumin rinjaye a zaben fitacciyar jihar North Rhein Westphalia da ya gudana a wannan Lahadi.
Jam'iyyar CDU mai mulki ta lashe kujerun majalisar jihar da kashi 34.5. Zaben na yau dai na zama zakaran gwajin dafin zaben gama gari da ke tafe a watan Satumba, bisa la'akari da muhimmancin jihar ta North Rhein mai mafi yawan al'umma da karfin tattalin arziki a Jamus.
Hakan kazlika ya karawa Merkel kwarin gwiwar fafutukarta na neman zarcewa a karo na hudu, a matsayin shugabar gwamnatin wannan kasa da ta fi ko wacce karfin tattalin arziki a Nahiyar Turai.
Nasarar CDU ya kawo karshen gwamnatin jami'iyyar SPD na Fremiya Hannelore Kraft, wadda kazalika ta yi murabus daga shugabancin jam'iyyar a wannan jiha.
Mutane miliyan 13 a cikin mazauna jihar ta North Rhine Westphalia miliyan 18 ne suka cancanci kada kuri'u, wanda ke wakiltar sama da kashi daya daga cikin biyar na yawan al'ummar kasar ta Jamus.