Cafke dan bindiga a Jamus | Labarai | DW | 10.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cafke dan bindiga a Jamus

Jami'an 'yan sandan kasar Jamus sun cafke wani mutum da ake zargi da harbe mutane biyu har lahira tare da budewa wasu daban wuta, sai dai bai samu nasarar kashe su ba.

Rahotanni sun nunar da cewa mutumin wanda kawo yanzu ba a bayyana ko wanene shi ba, ya harbe wata mata a kudancin Jamus a safiyar wannan Jumma'a da misalin karfe tara da mintuna 30 agogon GMT ta hanyar harbin ta daga cikin motarsa kirar Marsandi a garin Tiefenthal kusa da Ansbach wadda kuma nan take ta ce ga garinkunan. Daga bisani ya karasa garin Rammersdorf da ke makwabtaka inda ya hallaka wani mutum da ke kan kekensa. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ta Jamus Simone Wiesenberg ta sanar da cewa mutumin ya kuma budewa wasu mutane wuta da kuma wani direban mota sai dai bai samu nasarar hallaka su ba, inda ta ce cikin dan lokaci kalilan rundunarsu ta samu nasarar cafke mutumin kana suna ci gaba da gudanar da bincike.