Bukukuwan sabuwar shekara cikin fargaba | Labarai | DW | 31.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukukuwan sabuwar shekara cikin fargaba

Kasashen duniya na shirin gudanar da bukukuwan shiga sauwar shekara cikin tsatsaurar matakan tsaro, sakamon yadda aka soma bangado shirin kai hare-hare na ta'addanci a cikin wasu kasashen.

A birnin New York na Amirka an shirya baza jam'ian tsaro da motocin sulke sama da 165 a dandalin da jama'a za su taru a yayin da a birni Berlin a kofar Brandenburg za a girke jami'n tsaro sama da dubu goma.Kana a Faransa kusan sojoji dubu dari za a baza a dandalin na wuraren da jama'a za su taru domin yin bukukuwan.Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merke da take yin jawabi ga al'umma kasar a albarkacin sabuwar shekara da ke shirin kamawa ta yi kira ga hadin kan al'ummar kasar domin yaki da ta'addanci.