Bukatar dora haramci akan jam′iyyar NPD ta Jamus | Labarai | DW | 05.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar dora haramci akan jam'iyyar NPD ta Jamus

Ministan harkokin cikin gidan Jamus, Hans-Peter Friedrich ya sake jan ka kafa game da bukatar dora haramci akan jam'iyyar NPD mai manufar kyamar baki

Ministan cikin gidan Jamus da ministocin cikin gida na jihohin kasar su gudanar da tataunawa akan bukta ora haramc akan jamiyar NPd mai manufa kyamar baki . a taron da suka gudanar agarin Rosctock Warne muende ministocin sun dace kan mika shawarar da ta dace ga taron taron gwamnonin jihohi. A gobe alhamis ne gwamnonin za su tsai da shawara kan shawarar da ministan cikin gida, Hans-Peter Friedrich ya bayar da cewar a dakatar da shirin sake shigar da bukatar dora haramci akan jam'iyyar NPD mai manufar kyamar baki. Friedrich ya ce yin hakan na tattare da hadarin ba da karin karfi ga jam'iyyar da ba ta samu karbuwa sosai ba. Ya kara da cewa mai yiwuwa ne duk wani mataki na dora haramci akan jamiyar ya dauki hankalin kafafen yada labaru. A don haka ana bukatar kauce ma hadarin da ke tattare da bukatar dora haramcin. A shekarar 2003 ne dai kotun tsarin mulkin Jamus ta fara mika bukatar dora haramci akan jamiyar ta NPD to amma sai ba ta yi nasara ba saboda cewa akwai kusoshin jam'iyyar da dama da ke aiki a matsayin jami'an kare kundin tsari mulki.

Mawallafiya:Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal