Buhari zai je duba lafiyarsa a London | Labarai | DW | 24.06.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari zai je duba lafiyarsa a London

A wannan Juma'a ce ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tafi Ingila domin binciken lafiyarsa, a cewar sanarwar da ta fito daga fadar gwamnati da ke Abuja.

Mai shekaru 78 da haihuwa, Buharin ya sha yin irin wannan balaguro don duba lafiyarsa a kasar ta Birtaniya, tun bayan hawan sa mulki a shekara ta 2015, duk da korafe korafe daga bangaren al'ummar kasar.

A watan Maris ne dai shugaban Najeriyar ya kai ziyara makamancin wannan a birnin London, tafiyar da yayi gabanin yajin aikin likitocin Najeriyar, saboda rashin isassun kayan aiki da albashi mai inganci.