1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Buhari ya yi tozali da sojojin da ke fagen daga

June 17, 2021

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba wa sojojin da ke bakin daga a yankin Arewa maso gabashin kasar tabbacin samar masu da isassun kayan yaki dan kawo karshen rikicin Boko Haram.

https://p.dw.com/p/3v7jW
Der nigerianische Präsident Buhari besucht den Bundesstaat Borno
Shugaba Muhammadu Buhari na sauraren sojaHoto: Bayo Omoboriowo

Da isar Shugaba Muhammadu Buhari a Borno ya zarce kai tsaye zuwa wuraren kaddamar da aiyukan da gwamnatin jihar Borno ta aiwatar, kamar jami’ar jihar Borno da makarantar horar da sana’o’i da ke yankin Muna da cibiyar kula da lafiya ta Abbaganaram da wata hanya a jiddari Polo da gidajen da ake shirin mayar da ‘yan gudun hijira da ke Kaleri. Shugaban ya kuma ziyarci dakarun tsaron Najeriyada ke yaki da Boko Haram, ya kuma gana da wadanda su ka ji rauni a filin daga, inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi dukkanin mai yiwuwa na samar mu su da kayayyakin yaki na zamani domin su murkushe aiyukan ta’addanci a wannan yankin da ma sauran sassan Najeriya.

Karin Bayani: Kalubalen sababbin hafsoshin tsaron Najeriya

Shugaban Najeriya ya ce gwamnati ba za ta aminta kasawa daga bangaren dakarun tsaron kasar ba musamman in an samar masu da ababen da su ke bukata, yana mai cewa "A matsayi na na babban kwamnadan dakarun tsaron kasa, zan baku tabbacin cewa wannan gwamnatin za ta ci gaba da samar maku da isassun kudade a kan lokaci da kuma samar da makamai, wannan na da manufar karfafa wa yakin da ake yi yanzu domin kawo karshen sa." To sai dai ba kowa ne ya gamsu da wannan alkawarin da shugaban ya yi ba na samar da kayan yaki ga dakarun sojan da ke yankin, inda wasu kamar Atiku Galadima wani mazaunin Maiduguri ke cewa sai sun gani a kasa.

Karin Bayani: Taro kan matsalar tsaro da ta mamaye Tafkin Chadi

Wasu al'ummar yankin da shugaban Najeriya ya ziyarta na ganin wannan ziyara ba ta haifar masu da komai ba sai kuncin rayuwa, saboda yadda jami’an tsaro suka takura wa mutane da hana wa jama'a zirga zirga. Abdulsalam Muhammad wani mai sana’a ya shaida cewa ya fuskanci matsalar sana'arsa a yayin wannan ziyarar ta Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Hukumomi a jihar Borno sun ce ziyarar ta yi nasara da ake nema inda suka ce jama’a sun fito sun tari shugaban wanda ya karkare ziyar ta sa a fadar Shehun Borno ya kuma koma gida Abuja.