Najeriya: Kalubalen sababbin hafsoshin tsaro | BATUTUWA | DW | 27.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Kalubalen sababbin hafsoshin tsaro

Nada sababbin manyan hafsoshin tsaro a Najeriya, na ci gaba da sanya murna a tsakanin al'ummar kasar da ke cike da fatan samun sauyi.

Nigeria Katsina | Präsident Muhammadu Buhari

Tabbatar da tsaro na daga cikin alkawuran da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi

Abin tambayar dai dangane da nadin sababbin hafsoshin tsaron a Najeriya shi ne: su wanene sababbin manyan hafososhin kuma wane kalubale ke gabansu a aikin samar da tsaro a kasar? Sabbin hafsoshin tsaron da  shugaban kasar Muhammadu Buhari ya nada dai, sanannu ne a fagen fama na yaki da ayyukan ta'adanci a kasar, domin kusan dukkansu an dade ana damawa da su a fagen fama, kana sun jima suna rike da manyan mukamai kafin kai wa ga wannan matsayi da yake shi ne kololuwar aikinsu na soja. 

Karin Bayani: Ceto 'yan Nijar daga 'yan bindiga a Katsina

Koda yake Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka mai ritaya, masani a fanin tsaro a Najeriyar da ya yi aiki tare da mafi yawan sabbin hafsohin, ya bayyana yadda yake kalon cancanatarsu, sai dai ga Kyaftin Sadeeq Garba Shehu mai ritaya kwarre a fanin tsaron shi ma, ya ce yaki fad an zamba ne.

Karikatur Cartoon Nigeria

'Yan Najeriya sun zuba idanu suka sauyin da sababbin hafsoshin tsaron za su kawo

Shugaba Muhammadu Buharin dai ya nada Leo Irabor a matsayin babban hafsan tsaron kasar sai Manjo Janar Ibrahim Attahir shugaban hafsoshin kasa na kasar. Sauran su ne Real Admiral A Z  Gambo shugaban rundunar sojan ruwa sai kuma Air Vice Marshal A.O Amao a matsayin shugaban rundunar sojojin sama. Sun dai kama aiki ne a daidai lokacin da ake doki da murna da ma kosawa da sauyin da ya kai su ga wannan matsayi mafi kololuwa a tsaron Najeriyar, saboda hasashe na samun canji a yadda ake gudanar da yaki da ta'adanci a Najeriyar da ma sauran matsaloli na rashin tsaro a kasar.

Karin Bayani: Majalisun Najeriya sun magantu kan tsaro

Dakta Kole Shettima manazarci a cibiyar dimukurdiyya da ci-gaban kasa da ya fito daga shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar, ya bayyana cewa akwai kalubale a gaban sababbin hafsoshin tsaron Najeriyar. Abin jira cike da fata da shi ne yadda sababbin hafsoshin tsaron za su bai wa marada kunya a kasar, a daidai lokacin da take fuskantar tarin kalubale ta fanin tsaro.

Sauti da bidiyo akan labarin