1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji da dama sun hallaka a Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
July 20, 2020

Wani harin 'yan bindiga ya hallaka sojan Najeriya 23 a kauyen Jibiya na Jihar Katsina a arewa maso yammcin Najeriya, yankin da ke fama da tashe-tashen hankula na 'yan bindiga da masu garkuwa da jama'a.

https://p.dw.com/p/3fZyg
Nigeria Soldaten patrouillieren in Tungushe
Hoto: AFP/Str

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito wani hafsan sojan Najeriya na cewa har yanzu da akwai wasu sojojin da dama wadanda harin ya rutsa da su da ba a ji duriyarsu ba baya ga wadanda aka hakikance sun hallaka. Wani dan kato da gora ya shedawa manema labarai cewa har zuwa yammacin ranar Lahadi an ci gaba da neman sauran sojan da suka bata, inda ya nuna fargabar ko adadin sojojin da suka gamu da ajalinsu ka iya karuwa.