Buhari ya gana da ′yan Chibok kafin fita zuwa London | Labarai | DW | 08.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ya gana da 'yan Chibok kafin fita zuwa London

Wannan fita zuwa London ta shugaban ta sake bude sabon babi na fargabar yanayi na rashin lafiya da yake fama da ita, rashin lafiyar da ba a sani ba har yau.

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban dan shekaru 74 ya yi jinkiri na tafiyar domin ya gana da 'yan matan Chibok 82 da aka sako daga hannun mayakan Boko Haram inda ya ce gwamnati za ta ba su kulawa ta musamman.

Tuni dai kungiyoyi da ke fafutikar ganin an kwato mutanen da ke hannun mayakan na Boko Haram suka bayyana ra'ayoyinsu dangane da kubutar wadannan 'yan mata, Enoch Mark uba ne ga 'yan mata biyu da ke hannun mayakan na Boko Haram:

"Shekaru uku ba wasa ba ne, idan ya kasance babu nawa cikin yaran me zan iya, za mu hadu mu taya wadanda na su suka kubuta murna, kana mu yi fata ga sauran su samu kansu."

Kafin wannan lokaci dai da Shugaba Buhari ya koma London, ya yi makonni uku a jere ba tare da halartar zaman majalisar zartarwarsa ba, abin da ya sake fito da rashin lafiya da shugaban ke ciki wacce har kawo yanzu babu takamaimai bayanai na sanin abin da ke damunsa.