1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani bayan gwamna Zulum ya tsallake hari

September 28, 2020

'Yan Najeriya na tofa albarkacin bakinsu kan jerin hare-haren da aka kai wa gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a karshen mako.

https://p.dw.com/p/3j88B
Afrika Nigeria Borno Professor Babagana Umara Zulum
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara ZulumHoto: Government House, Maiduguri, Borno State

Jami'an tsaro 18 ne dai suka rasa rayukansu yayin wadannan hare-haren da aka kai wa ayarin motocin gwamnan na Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum kamar yadda shelkwatar sojojin Najeriyar ta yi karin haske, inda ta ce ta samu damar dakile hari.

Karin Bayani: Fargabar sansanonin Boko Haram a Abuja

Tun bayan samun labarin kai jerin hare-haren kan ayarin motocin gwamnan na jihar Borno 'yan Najeriya ke nuna damuwa, musamman ganin yawan jami'an tsaron da su ka rasa rayukansu a harin. Yayin da wasu ke zargin sakacin gwamnati da jami'an tsaro wasu kuma na ganin cewa abun ya wuce tunanin dan Adam.

Karin Bayani: An dakatar da ayyukan agaji a Najeriya

Nigeria | Niedergebrannte Fahrzeuge in Auno
Hare-haren ta'addanci na karuwa a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/A. Marte

A fili yake dai cewa yawancin 'yan Najeriya sun shiga damuwa saboda wannan hari da suka ce ya sake fito da matsalolin tsaro da ake ciki. Malam Adamu Dan Borno wani mazaunin Maiduguri, na ganin gazawa ce daga bangaren gwamnatin tarayya da jami'an tsaron Najeriyar.

Karin Bayani: Boko Haram ta kai hari kan sansanin soja

Ganin yadda rayuwar gwamnan ke kara fadawa cikin hadari, wasu na ganin ya kamata gwamman ya dakatar da irin wadannan tafiye-tafiye har an samu ingantuwar tsaro a yankunan. To ammm ga Sale Bakuro shugaban kabilar Kare-kare mazauna Damaturu na ganin bai kamata

hare-haren  da ake kai wa gwamnan su sa shi ya yi kasa a gwiwa ba. A kashin kansa dai gwamna Babagana Umara Zulum ya ce, a shirye yake ya rsa ransa in dai za a samu zaman lafiya 'yan gudun hijira su koma gida kuma harkokin rayuwa su dawo a jihar ta Borno, wacce a baya ake mata kirari da cibiyar zaman lafiya.