1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadari a komen 'yan gudun hijirar Borno

December 21, 2021

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch, ta yi gargadi kan hadarin da ke tattare da mayar da 'yan gudun hijira garuruwansu a jihar Bornon Najeriya.

https://p.dw.com/p/44dk6
Nigeria | Wasserknappheit in Maiduguri
Dubun-dubatar mutane matsalar tsaro ta tilastawa gudun hijira a jihar BornoHoto: Gilbertson/ZUMAPRESS/picture alliance

Gargadin kungiyar ta Human Rights Watch mai rajin kare hakkin dan Adam dai, ka iya dakatar da kokarin mayar da 'yan gudun hijirar jihar ta Borno zuwa garuruwansu na sali. Ya zuwa karshen makon gobe ne dai hukumomin jihar ta Borno, suka ce suna shirin kamalla kwashe kusan mutane miliyan biyu da ke gudun hijirar domin komawa garuruwansu.

Karin Bayani:n Makomar tubabbun 'yan Boko Haram

To sai dai kuma daga dukkan alamu, aikin komen na daukar hankalin hukumomi da kungiyoyi masu rajin kare hakkin dan Adam da ke fadin akwai barazana mai girma  a cikinsa. Ta baya-bayan dai, na zaman kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Human Rights Watch da ta ce 'yan gudun hijirar na fuskantar barazana babba daga mai da su gidan ko ta halin kaka. A fadar jami'ar kungiyar a Tarayyar Najeriya Aniete Ewang kuskure ne babba, a raba mutane da muhallinsu ba tare da an samar musu zabi mai inganci ba.

Nigeria Region Borno Boko Haram
Har yanzu ana ci gaba da kai hare-hare a sassa dabam-dabam na jihar BornoHoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

A cikin watan Agustan bara ne dai, gwamnatin jihar Bornon ta ce ta tanadi matsugunai domin sake mayar da 'yan gudun hijirar da suka share shekaru a dokar daji zuwa gida. Shirin kuma da ke fuskantar suka, ta gaza biyana bukatun 'yan hijirar yanzu. Hadiza Bello dai na zaman daya a cikin masu gudun hijirar da gwamnatin jihar ta mayar Goza, kuma ta ce rayuwa ba dadi cikin sabon matsugunin da take ciki a halin yanzu.

Karin Bayani: Yunwa ta sa 'yan gudun hijirar Borno fusata

Ko bayan gazawa ta muhallin dai, ana kuma fuskantar karuwar hari a sababbin yankunan da hukumomin ke fatan za su zamo wuraren rayuwar al'umma. Duk da ikirarin jami'an tsaron Najeriyar dai, har ya zuwa yanzu ana kallon tashi da lafawar hari cikin jihar daga kungiyar ISWAP ta ta'adda. Abun kuma da a cewar Kabiru Adamu da ke sharhi kan al'amuran tsaro, ya sanya da kamar wuya a iya kai wa ya zuwa nasara a cikin shirin na sake mayar da mutane zuwa gida.