1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafita kan yanayin tsaro a Najeriya

August 24, 2021

A yayin da ake ci gaba da takaddama kan makomar daruruwan 'yan kungiyar Boko Haram da ke ta mika wuya, ya zuwa yanzu gwamnan jihar Borno da shugaban Najeriya sun gana da nufin sanin mataki kan makomar tsofaffin mayakan.

https://p.dw.com/p/3zRKg
Nigeria Region Borno Boko Haram
Matsalolin tsaro sun yi wa Najeriya dabaibayi, musamman a yankin arewaciHoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan na Borno Babagana Umara Zulum dai, sun share lokaci suna wata ganawar sirri domin nazarin mika wuyan na 'yan kungiyar ta Boko Haram din na ba zata. An dai kammala wannan tattaunawa, inda gwamnan jihar Bornon ya bayyana cewa, bangarorrin biyu sun amince da wani tsari da a cewarsa ka iya kawo karshen ayyukan kungiyar. Farfesa Zulum dai ya ce kimanin kaso 10 cikin 100 na daukacin al'ummar Borno sun tsere daga gidajensu, ko bayan illa ga tattalin arziki da zamantakewar al'ummar jihar. Abun kuma da a cewarsa ya sanya jihar ba ta da zabi  face ta rungumi masu mika wuyan da nufin samun zaman lafiya tsakanin al'ummar jihar.

Cartoon Baba Nigeria
Al'ummar Najeriya dai, na cikin fargabar rashin tsaro

Kasawa da kokarin mika wuya ko kuma tsoro na wuta ta kaikayi, ana dai shirin kai ruwa rana tsakanin gwamnatin da ke fadin ta karba da kuma wadanda kungiyar tai wa illa da ke fadin ba hali. To sai dai kuma a cewar Zulum Abujar da ma ita kanta jihar Borno, na shirin tantancewa da nufin yin adalci ga kowa. Koma ya take shirin da ta kaya a tsakanin masu neman afuwar da masu bukata ta hukunci kan laifin na ta'adda, can a jihar Plateau da ke kokarin kwantar da hankula sakamkon rikicin da ke shirin ballewa, gwamnan jihar ya ce kotu ce za ta raba tsakanin masu kisa a jihar. Simon Lalong dai ya ce ba hujjar sakin kamammun Rukuba da ma ragowar da ke da ruwa da tsaki da tayar da hankulan al'ummar jihar. Tarayyar Najeriyar dai, na neman mafitar jerin rigingimun rashin tsaron da ke sauyin launi cikin kasar da ma barazana ga zabukan kasar  da ke kara karatowa.