Boko Haram ta kashe wasu sojojin Najeriya | Labarai | DW | 16.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kashe wasu sojojin Najeriya

Dakarun gwamnatin Najeriya shida sun mutu a wani sabon harin kwantar bauna da mayakan jihadi suka kaddamar kan ayarinsu a kusa da kauyen Mayanti da ke kusa da iyaka da Kamaru.

Kamfanin dillancin labarun Faransa AFP ya samu tabbacin faruwar harin yayin da sojojin ke hanyar zuwa kusa da garin Banki.

Duk da ikirarin gwamnatin Najeriya da rundunar tsaron kasar na samun galaba kan mayakan Boko Haram, Majalisar Dinkin Duniya na damuwa kan yadda maharan ke cigaba da dauki ba dadi da kuma halaka mutane.