Boko Haram ta kai hari kusa da Chibok | Labarai | DW | 25.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kai hari kusa da Chibok

A Najeriya a yayin da ake dab da soma bukukuwan kirismeti wasu mayakan da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane bakwai tare da yin garkuwa da yarinya daya

Wasu maharan da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai wani hari a wani kauye na mabiya addinin Krista da ke kusa da Chibok tare da hallaka akalla mutane bakwai da kuma yin garkuwa da wata budurwa daya.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ruwaito wani mai suna David Bitrus ma zauni garin na Kwarangulum da ke da tazarar kilo mita 16 daga Chibok na cewa maharan sun kai harin ne a jiya tare da kona wata cocin garin da wasu gidaje, kana kuma suka dibi kayayakin cimaka da dama.