Boko Haram ta hallaka mutum 11 a Gomboru
January 3, 2018Talla
Wani dan kunar bakin wake ya halakka mutane goma shadaya a wani harin bam da ya kai a masallaci da safiyar laraba a yankin Gamboru na Jihar Borno a Najeriya da ke iyaka da kasar Kamaru.
Jami'an soji da na bada agaji sun tabbatar da cewa maharin ya tada bam din ne a lokacin da ake gudanar da sallar asuba..
Kungiyar Boko haram ta saba amfani da 'yan kunar bakin wake musamman mata da kananan yara wajan kai hare-hare a wuraren taron jama'a musamman kasuwanni da wuraren ibada.