Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo | Labarai | DW | 14.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo

Wani sabon faifayen bidiyo da kungiyar Boko Haram din ta fitar, ya nuna wasu daga cikin ‘yan matan sakandaren Chibok da take garkuwa da su sama da shekaru biyu tare da barazanar hallakasu.

Sabon Faifayen bidiyo kan 'yan matan Chibok na Najeriya

Sabon Faifayen bidiyo kan 'yan matan Chibok na Najeriya

An nuno wani daga cikin mayakan kungiyar tsaye a gaban yan matan masu yawa inda ya ce ba su da wata bukata da yan matana illa a sake musu yan uwansu kafin su sake su. Ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin wadannan yan matan sun mutu sanadiyyar luguden wuta ta sama da jirgen sojoji suka yi a kan 'yan kungiyar. Ya kuma bayyana cewa akwai wasu daga cikin 'yan matan da ke jinya, inda wasu kuma kusan 40 ya ce sun yi aure. An nuna daya daga cikin yan matan wacce ta yi magana da hausa da kuma yaren 'yan Chibok inda ta yi kira ga iyayensu, da su yi hakuri kuma su nemi gwamnati ta saki 'yan Boko Haram din da take tsare dasu domin suma su samu a sake su.