Boko Haram ta dauki alhakin sace ′yan mata a Najeriya | Labarai | DW | 05.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta dauki alhakin sace 'yan mata a Najeriya

A wani faifayen video da ya fitar shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya sanar cewa sune suka sace yan mata yan makaranta a Chibok

Kungiyar Boko Haram ta sanar cewa ita ce ke da alhakin sace 'yan matan nan 276 daga makarantar 'yan mata ta garin Chibok dake arewa maso gabacin kasar ta Nageriya.

Cikin wani faifayen bidiyo da ya dauki akalla mintuna 57, shugaban wannan kungiya Abubakar Shekau ya ce su ne suka sace 'yan matan, kuma za su sayar da su a matsayin bayi, kuma su aurar da su da karfi.

Tuni dai da ma a wasu labaran da ke yaduwa, aka ce akwai yiwuwar ketarawa da wadannan 'yan matan ya zuwa kasashen Chadi da Kamaru, masu makwabtaka da wannan da Najeriya, inda ma aka sayar da ko wace yarinya, a kwatankwacin dala goma sha biyu ta Amirka.

A wannan sabon faifayen bidiyon dai Shekau na sanye ne da kayan soja, kuma yana tsaye gaban wasu motoci masu dauke da kayan yaki, inda yake kewaye da wasu mutane guda shidda dauke da makammai.

Mutanen dai suna magana ne da Hausa, da Larabci, da kuma turancin Inglish, kuma fuskokin su a rufe.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal