Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya | Labarai | DW | 12.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya

Wasu sojoji kasar Najeriya sun salwanta, a lokacin da wasu mayakan Boko Haram ne suka yi masu kwantan bauna a wani bangare na sansanin Sambisa da ke kan iyakar kasar da jamhuriyar Kamaru.

Rahotanni daga Najeriya, na cewa akalla sojojin kasar uku sun salwanta a lokacin da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka yi masu kwantan bauna a wani bangare na sansanin Sambisa da ke kan iyakar kasar da Kamaru. Wasu majiyoyi ciki har da na jami'an tsaro, su ne suka shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP na Faransa faruwar lamarin, inda suka ce wani mayakin na Boko Haram ma ya rasa ransa.

Harin dai ya auku ne lokacin da sojojin ke hanyarsu ta komawa sansaninsu aJuma'ar da ta gabata, a dazukan Gwoza da ke cikin jihar Borno. Akwai kuma wasu sojoji 10 da wani dan kato da gora da suka jikkata. Bayanai sun ce sojojin sun yi nasarar kiran jiragensu na yaki, wadanda suka kawo dauki cikin gaggawa da ya kaiga murkushe harin.