Boko Haram na neman farfadowa a Najeriya | Labarai | DW | 15.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram na neman farfadowa a Najeriya

Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a Tarayyar Najeriya sun kai wani hari a wajen garin Maiduguri babban birnin jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Rahotanni sun nunar da cewa maharan sun kai farmaki da misalin karfe uku na wannan Jumma'a a agogon Najeriya karfe biyu ke nan agogon GMT. Harin wanda aka kai a wajen birnin na Maiduguri a wani guri da aka sake tsugunar da mutanen da rikicin kungiyar ta Boko Haram ya tarwatsa da ke da nisan misalin kilomita 10 da garin na Maiduguri.

Kawo yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ko kuma suka jikata a wannan harin ba wanda ke zaman na biyu cikin wannan makon da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai a Maidugurin fadar gwamnatin jihar Borno.