Boko Haram: Janye yara daga aikin samar da tsaro | BATUTUWA | DW | 18.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Boko Haram: Janye yara daga aikin samar da tsaro

Rundunar matasan nan da ke taimakon jami'an tsaro yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya da aka fi sani da Civilian JTF ta rattaba hannun da majalisar Dinkin Duniya na cire yara daga aikin tabbatar tsaro.

A baya dai majalisar dinkin duniya ta sanya sunan rundunar matasan CJTF cikin wadan ke amfani da yara a matsayin Sojoji da ke aikin tabbatar tsaro lamarin ya saba da yarjejeniyar da kasasehn duniya suka amince da ita na hana amfani da yara a yyukan Soji.

Domin tsarkake sunan rundunar tare da tabbatar suna aiki bisa ka'idoji da kasashen duniya suka amince da su ya sa rundunar rattaba hannu a wata yarjejeniya da Asusun kula da yara na majlisar dinkin diniya wato UNICEF na wanda zai tabbatar da cire yara da shekarun su bai kai 18 daga ayyukan Kungiyar.

An rabbata hannun a idon Mataimakin gwamnan Jihar Borno Alhaji Usman Mamman Durkwa da kuma babban jami'in Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, da ke Najeriya Mohamed Fall wanda ya taya murna ga rundunar saboda wannan wannan babban mataki da ta dauka saboda kare yaran arewa maso gabashin Najeriya.

Ita dai rundunar ta CJTF ba ta amince tana daukar yara a aikin tabbatar da tsaron ba, ta ce matukar bai cika shekarun girma na shekaru 18 ba. A cewar ta yaran kan sa kansu yin wannan aikin ne ba tare da sanin rundunar ba kuma daga yanzu ba za ta sake barin kowane yaro ya sa kansa a wannan aiki ba.

A cewar Barista Jibrin Gunda jami'in kula da harkokin shari'a na rundunar uun amince da rattaba hannun kan wannan yarjejeniya domin tabbatar da an cire sunan rundunar daga sunayen rundunonin da Majalisar Dinikin Duniya ke zargin suna daukar yara aikin soji.

Labarin rattaba hannun ya yi wa iyaye masu rajin kare hakkin yara dadi wanda suka ce haramta yara shiga irin wadan nan ayyukan zai taimaka gaya wajen gyara tarbiyar yaran da kuma ba su damar zuwa makaranta. Comrade Lucy Yunana uwa ce kuma mai rajin kare hakkin yara a Najeriya wadda ta yaba da matakin. Masharhanta na neman ganin rundunar za ta aiwatar da wannan yarjejeniya tsakani da Allah a Maiduguri da sauran sassan Jihar Borno da jihohi makobta.

Sauti da bidiyo akan labarin