Boko Haram: Buratai zai koma Maiduguri | Labarai | DW | 28.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram: Buratai zai koma Maiduguri

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya umarci shugaban sojin kasar Yusuf Tukur Buratai da takwaransa na sojin sama da su koma jihar Borno da ke arewacin kasar don karfafa yakin da ake da Boko Haram.

Wannan umarni na shugaban ya biyo bayan kisan soji 9 da wasu fararen hula da dama aka yi bayan wani kwanton bauna da 'yan Boko Haram din suka yi wa sojin kasar a kokarinsu na kwato masu binciken kasa na kamfanin mai na kasar da wasu malamai na jam'iar Maiduguri da Boko Haram din suka yi garkuwa da su a kwanakin da suka gabata. Tuni dai ma'aikatar tsaron kasar ta bakin ministanta Janar Mansur Dan Ali mai ritaya ta ce ta matsa kaimi a yaki da Boko Haram din musamman ma dai a wannan lokaci da suke zafafa kai hare-hare.