Boka Haram: Mahawara kan makomar Shekau | Siyasa | DW | 04.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Boka Haram: Mahawara kan makomar Shekau

Sojin Najeriya suna ikirarin irin nasarar da suke samu a cikin yakin da ya kalli sauyi na kwamandoji da ma dabaru a cikin kasa da wattani biyun da suka gabata.

To sai dai a daya bangaren ita ma kungiyar har yanzu ba ta kai ga yin la'asar ba a cikin yakin da ya kalli karuwa ta hari na kuna ta bakin wake a bangare na kungiyar da ma kokari na kai kai hari na na isa zuwa wasu sassa na jihar Borno.

To sai dai kuma mafi dauka ta hankali ya zuwa yanzu na zaman wani fefen bidiyon da 'yan kungiyar suka kai ga fitarwa ya zuwa yanzu, Bidiyon kuma da a karo na biyu ke dauke da hoton wani mutumin da ke zaman daban daga Shekau din al'ada.

Abun kuma da tuni ya fara jawo muhawara ta makomar jagora na kungiyar da ya share shekara da shekaru yana amo ana amsawa amma ya kai ga bacewa ta ba zata a cikin yakin.

Duk da cewar dai babu sahihai na rahotanni game da makomar Shekau din dai daga dukkan alamu sauyin fasalin yakin ya fara nuna alamun tasiri a cikin rikicin na shekaru shida da kuma yanzu haka sabbabin mahukunta na kasar ke dada samun kwarin gwiwa kansa.

Hosea Sambido dai na zaman shugaban kungiyar al'umar Chibok da ke a Abuja, mutumin kuma da ya dawo daga yankin a cikin mako ya kuma ce rayuwa ta sauya kuma hankali yana nuna alamar kwantawa a tsakanin al'ummarsu.

Kokari na sake rayuwa cikin Chibok, ko kuma ci gaban tada hankali dai tuni sojojin kasar suka ce sun sake bude tituna da kwace garuruwa daban daban cikin jihohin Borno da Yoben dake zaman fagen famar yakin ya zuwa yanzu, kuma suna samun gagarumin nasarar da ta kaisu har ga shiga dajin Sambisa a halin yanzu.

Daruruwan 'ya'yan kungiyar ne dai sojan kasar ta Jajeriya suke fadi sun kai ga hallkawa, sannan kuma da wasu daruruwan na al'ummar yankin da sukai nasarar kubutowa daga hannu na kungiyar.

To sai dai kuma a tunanin Dr kole Shettima dake zaman shugaban cibiyar demokaradiya da ci gaba da kuma ke bin diddigin yakin ya zuwa, duk wata nasara ko dai a banagre na kungiyar ko kuma a wurin sojojin zata kammala ne tare da komawa bisa teburi na Shawara da nufin tattaunawa a tsakanin juna.

Akwai dai rade radin bude hanyar tattaunawa a tsakanin Abujar da kuma 'yan gwagwarmayar Sambisan da ke a tsakanin sulhu d agwamnatin da kuma fuskantar yanayi mara tabbas sakamakon sauyin rawa a bangare na makwabta da kuma taimako na makaman tarawa ga Abujar.

Akwai sautin rahoton daga kasa.

Sauti da bidiyo akan labarin