1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binne gawa

Adrian Kriesch / ASJanuary 14, 2015

Kwayoyin cutar Ebola na da hatsari ko a jikin gawa.

https://p.dw.com/p/1EGjx
Sierra Leon Ebola Beerdigung Opfer 14.08.2014
Hoto: AFP/Getty Images

Kwayoyin cutar Ebola na cigaba da kasancewa da karfi a jikin mutumin da cutar ta hallaka don haka bai kamata a taba gawarsu ba. A yammacin Afrika mutane da dama sun kamu da cutar ne yayin irin al’adun da ake yi na jana’izar wanda cutar ta hallaka. Irin wadannan al’adu sun hada da sumbata da wankewa ko taba gawa don haka yana da kyau a kasance da nisan akalla mita guda daga gawar wanda ya rasu sakamakon kamuwa da Ebola.

Yana kuma da kyau a kone katifa da kaya da sauran abubuwan da mamaci ya yi amfani da su kafin cutar ta Ebola ta yi ajalinsa domin yin hakan zai taimaka wajen rage bazuwar kwayar cutar.

Dangane da binne mamaci kuwa, yana da kyau a bar kwararru su yi hakan. A kasar Gini da Liberiya da Saliyo hukumar bada agaji ta Red Cross ta na da jami‘an da aka horar don yin wannan aikin kuma za a iya kiransu ta irin layukan nan na kar-ta-kwana don binne mamaci. Su kan yi amfani ne da jakar leda da ake sanya gawa a ciki maimakon akwatin gawa ko makara wajen binne mamaci ko kone gawarsa.

Wadannan jami’an kan gudanar da aikinsu yadda ya kamata kuma su kan yi shi ne tare da mutunta gawar wanda cutar ta hallaka kuma ma sun samu horo kan yadda ake binne Kirista ko Musulmi cikin girmamawa.