Binciken tauraruwa mai wutsiya na kasashen Turai ya kankama
November 12, 2014Bayan kwashe miliyoyin mila-milai daga wannan duniya tamu yana tafiya a sararin samaniya kumbon binciken kasashen Turai ya saki mutummumin da zai yi bincike a tauraruwa me wutsiya Comet a Turance ta yadda za a rika samar da bayanai da za su hada da lalubo yadda duniya ta samo asali.
Paolo Ferri, shi ne jagoran wannan shirin binciken samaniya a Jamus:
Ya ce "Mun riga mun samar da banbanci kuma mun kafa tarihi da nasara".
Masu binciken a cibiyar samaniya Darmstadt a Jamus na samun bayanan saukar wannan mutum mutumi sun shiga murna.
To ko wannan nasara me take nufi a duniyar binciken kimiyar samaniya? Farfesa Yusuf Adamu masani ne na kimiyar muhallin dan 'Adam a jami'ar Bayero da ke Kano a Najeriya:
"Wannan na iya sauya tunanin mu kan asalin yadda duniya ta samo asali."
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo