Bincike bisa matsananci ra′ayi a rundunar sojan Jamus | Labarai | DW | 18.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bincike bisa matsananci ra'ayi a rundunar sojan Jamus

Ana bincike bisa matsanancin ra'ayi a rundunar sojan Jamus bayan sahidun gani da ido sun tabbatar.

Masu gabatar da kara na Jamus suna binciken game da yuwuwar samun wadanda suka yi alama irin na matsananci ra'ayi lokacin liyafar sojoji cikin watan Afrilu a garin Tübingen, inda ake cewa akwai wadanda suka alamun gaisuwa kamar na lokacin mulkin Adolf Hitler.

Haka ya kara kaimin badakala cikin rundunar sojojin Jamus inda a watan Afrilu aka cafke wani soja da ake zargi yana kitsa harin kunar bakin wake cikin cibiyar 'yan gudun hijira na Siriya. Tuni lamarin ya haifar da matsin lamba tsakanin ministan tsaron Jamus Ursula von der Leyen da kuma manyan hafsoshin soja.