Bikin tunawa da yaƙin duniya na biyu | Labarai | DW | 13.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin tunawa da yaƙin duniya na biyu

Jamus na gudanar da bukukuwa na nuna juyayi cikkar shekaru 70 da ƙasashe ƙawaye suka yi luguden wuta a Dresden a lokacin yaƙin duniya na biyu.

A lokacin faɗan na yaƙi da gwamnatin Hitler wanda jiragen sama na yaƙi sama da dubu uku suka jefa bama-bama dubu 650 an yi kaca-kaca da birnin. Wanda a sakamakon yaƙi kusan mutane dubu 25 suka mutu

An shirya a yau za a gudanar da aduo'i a cikin wani Coci a birnin na Dresden tare da halarta shugaban kasar ta Jamus domin tunawa da waɗanda suka mutu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar