Bikin tunawa da yaƙin duniya na biyu
February 13, 2015Talla
A lokacin faɗan na yaƙi da gwamnatin Hitler wanda jiragen sama na yaƙi sama da dubu uku suka jefa bama-bama dubu 650 an yi kaca-kaca da birnin. Wanda a sakamakon yaƙi kusan mutane dubu 25 suka mutu
An shirya a yau za a gudanar da aduo'i a cikin wani Coci a birnin na Dresden tare da halarta shugaban kasar ta Jamus domin tunawa da waɗanda suka mutu.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar