Bikin tunawa da Günter Grass a Lagos | Zamantakewa | DW | 01.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bikin tunawa da Günter Grass a Lagos

Shi dai Günter Grass daya ne daga cikin shahararrun marubutan adabi na Jamus wanda ya rasu bayan da ya yi ta fama da rashin lafiya.

Marubata da dama ne dai a Najeriya suka halarci bikin tunawa da marubshi Günter Grass, bikin da cibiyar raya al'adun Jamus ta Goethe abirin Lagos ta dauki nauyin gudanarwa

Shi dai marigayin da ya taba lashe lambar yabo ta Nobel a fannin adabi, shi ne marubucin kasar Jamus da ya fi samun karbuwa a kasashen duniya.

Shi dai Günter Grass mutum ne ba a rabawa da shaye-shaye na barasa da kuma lofe a rayuwarsa. Saboda haka ne ya yi ta amfani da duk damar da 'yan siyasa suka bashi wajen yin barkwanci a kan shan lofe.

"Ina so in bawa 'yan siyasa shawarar shan lofe kafin su furta wasu kalamai a bainar jama'a."

Baiwa daga Ubangiji

Baya ga rubuce-rukucen litattafai da kuma wakoki, Günter Grass ya kuma yi fice a sigar sassake-sassake da kuma zane-zane. Duk ma dai da baiwar da Allah Ya bashi, ba kowa ba ne yake iya fahimtar sakwannin da ke cikin rubuce-rubucensa cikin sauki. Ko da mista Grass ya bayyana cewar rubuce-rubucensa kukan kurciya ne wanda masu iya magana kan ce jawabi ne.

Wole Soyinka

Wole Soyinka, daya daga cikin marubuta a Najeriya

"A gaskiya a kowanne daga cikin sabbin jimlolin da na gina, sai idan mutum ya nitsu sosai zai gane inda na sa a gaba. Wadanda hankalinsu bai zarta wadanda har yanzu ke shan nonon uwarsa, ba sa cikin rukunin wadanda za su gane alkiblar da aka dosa."

Dawainiyar iyali musamman ma 'ya'ya da jikoki na daga cikin abubuwan da marubuci Günter Grass ke matikar kauna. Shi da mai dakinsa sun shafe wani bangare na rayuwarsu ne a garin Lübeck. Ma'abocin salon kida na Jazz ne da kuma rawar Tango. A cikin shekarun 1950 ma dai ya dan taba kida da waka.

"Mun rinka kida so biyu zuwa so uku a kowane mako, musamman da daddare, lamarin da ya ba mu damar samun dan abin rike aljihu. Mun hada kai karkashin wata kungiyar mawaka da muka kafa."

Taka rawa a fagen siyasa

Daga bisani ne Günter Grass ya karkata ga harkokin siyasa, inda ya kai ga taimaka wa tsohon shugaban gwamnatin Jamus Willy Brandt yakin neman zabe, tare da sa jam'iyyarsu ta SPD samun karbuwa a tsakanin al'umma. Ko da tsohon shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder wanda shi ma karkashin wannan jam'iyya aka zabeshi, sai dai ya yaba irin gudunmawar da marubuci Grass ya bayar lokacin da ya bashi lambar girmamawa a shekara ta 2012.

"Ficeccen Bajamushe, daya daga cikin wadanda muka fi alfahari da su a cikin shekaru goma na baya-bayannan da ma dai wannan karni da muke ciki. Ina farin cikin kasancewarsa a nan. Na fada masa cewar yana daga cikin mutanen da nake matikar kaunar rubuce-rubucensu saboda shahararre ne a iya shagube. Da ma mene ne amfanin fasaha idan ba shagube a ciki?"

Shi dai Günter Grass an haifeshi ne a ranar 16 ga watan Oktoba na shekarar 1927 a garin Danzig. Iyayensa marasa galihu ne, sannan ya taso ne a lokacin yakin duniya. Ya yi ta gwagwarmaya daga bisani don ganin cewa Poland da Jamus sun dinke barakar da ke tsakaninsu. Ya yi ta tir da ayyukan 'yan Nazi, sai dai kuma a shekara ta 2006 ya bayyana a cikin wani littafin da ya rubuta cewa shi tsohon mamba ne na kungiyar baradan Hitler.

"Ni ban taba daukar wannan a matsayin wani laifi ba saboda na girma ne a wannan yanayi na yaki a shekarun 1945. Daga bisani ma ban taba neman sannin me ya sa wannan batu yake ci gaba da daukar min hankali ba."

A shekara ta 2011, marubuci Günter Grass ya shiga cikin kanun labarai, inda aka zargeshi da mai kyamar Yahudawa bayan da a rubuce-rubucensa ya yi amfani da zafafan kalamai wajen sukar Isra'ila. Duk da cewa ya rigamu gidan gaskiya, amma dai abin da ba za a taba mantawa game da Grass ba shi ne lambar yabo da Nobel da ya samu a fannin adabi.

Sauti da bidiyo akan labarin