1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin mulkin demokradiyya a Najeriya

September 15, 2021

Ga dukkan alamu har yanzu da sauran tafiya a tsakanin miliyoyin al'ummar tarrayar Najeriya da biyan bukata a tsarin demokradiyyar kasar da ke tangal-tangal.

https://p.dw.com/p/40MJh
Nigeria Democracy Day 2019
Hoto: Reuters/A. Sotunde

An dai share tsawo na lokaci ana gwaji ana sakewa, to sai dai kuma daga dukkan alamu har yanzu da sauran tafiya a tsakanin miliyoyin al'ummar tarrayar Najeriya da biya na bukata a tsarin demokaradiyyar kasar da ke tangal-tangal. Kama daga APC mai mulki ya zuwa ita kanta PDP ta adawar  demokaradiya a cikin tarrayar Najeriyar dai na zaman karatu na gwaji da kokarin sakewa.

Karin Bayani: Gwamnati ta yi biris da kisan masu zanga-zanga

Kuma rikicin neman ikon fada a saurara ko ba dadi, game da bambancin addini da kabila, dama uwa uba cin hanci dai, shekaru 20 da doriya na sake girkin tsarin daga dukkkan alamu sun gaza kai wa ya zuwa girman tsarin balle balagarsa domin amfanina 'yan kasar dama bakinta.

Karikatur: Nigeria Politik
Hoto: A. Baba Aminu

A takarda an nisa a kokarin girka duma na demokaradiyyar don kowa, to sai dai kuma a zahiri tarrayar Najeriyar kuma a tunanin Ghali umar na'abba da ke zaman tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriyar na kallon wani tsarin da ke kama da kama karya.

“Kama karyar gwamna ko kuma kokari na shugabanci a cikin sabon tsarin dai ana kallon baba-kere na kalilan da kasa kai wa ga bukatar talakawan da ruwa da tsaki da tushen farko na ginin demokradiyyar a cikin tarrayar Najeriya''.

Karin Bayani: Najeriya: Mahawara kan sabuwar ranar demokradiyya

Sojoji ne dai suka raini sake dawowar tsarin ko bayan kafa kundin tsarin mulkin da ya bada karfi a bangaren zartarwa. Hasali ma dai sun nada nasu domin jagorantar sabuwar tafiyar da ke zaman mafi tsawo a Najeriyar ya zuwa yanzu. Fagen siyasar Najeriyar dai ya dau harami a cikin neman sake samun alkiblar da ke iya kai wa ga inganta rayuwar al'umma a gaba.