1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden: NATO ta kara karfi fiye da yadda ta ke a baya

Abdullahi Tanko Bala
February 21, 2023

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Ukraine na kan turbar 'yanci da walwala yayin da a waje guda yace NATO ta kara karfi fiye da yadda ta ke a baya.

https://p.dw.com/p/4NoEd
Polen Rede US-Präsident Biden
Hoto: Radek Pietruszka/PAP/dpa/picture alliance

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta kara karfi sosai fiye da yadda ta ke a baya.

Ya baiyana hakan ne a yayin ziyararsa a POland gabanin cika shekara guda da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

Biden ya shaida wa takwaransa na Poland Andrzej Duda kwana guda bayan ziyarar ba zata da ya kai birnin Kyiv.

Shugaba Biden ya bukaci makwabtan Ukraine su tallafa wa kasar a yakin da ta ke yi da Rasha yana mai cewa Ukraine na kan turbar 'yanci da walwala.

A ranar Laraba Biden zai gana da shugabannin kasashe tara na kungiyar kawancen tsaro ta NATO