1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bekele: Daga yari zuwa ga yaki da danniya

Maria Gerth ZUD/MAB
November 18, 2021

Shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Habasha Daniel Bekele ya lashe kyautar gwarzon mai kare hakkin dan Adam da Jamus ke bai wa 'yan fafutukar Afirka. Amma a kasarsa ba kowa ne ke yaba wannan girmamawar ba.

https://p.dw.com/p/43ALn
Äthiopien Addis Ababa Daniel Bekele Äthiopische Menschenrechtesbeauftragter
Hoto: Yohannes G/Egziabher/DW Addis Ababa

A matsayinsa na shugaban hukumar yaki da cin zarafin bil Adama mallakin gwamnatin Habasha, lauya Daniel Bekele, na shan suka kan yadda ya iya fitowa baro-baro ya nuna cewa gwamnatin da yake yi wa aiki na tabka kura-kurai. Tun kafin a nada shi mukamin da yake kai yanzu, kwararren lauyan ya yi aiki a matsayin dan fafutukar kare hakkin bil Adama.

Cin zarafin dan Adam da Bekele ya shaida tun  farkon rayuwarsa a Habasha ne ya sanya masa kwarin gwiwar kawo sauyi. Ya ce "Na taso a lokacin da Habasha ke karkashin mulkin danniya na soja, inda aka kulle mutane a gidan kaso, aka kuma kashe na kashewa ba tare da shari'a ba. Da idona na shaida yadda aka daure mahifina da mahaifiyata a gidan kaso. Daga nan sai 'yan tawaye suka kifar da mulkin sojar, mun dauka mun samu sauki ke nan, sai kawai Habsaha ta sake fadawa cikin wani sabon cin zali na siyasa.''

Zaman gidan yari ya yi tasiri a rayuwar Bekele

Äthiopien | Premierminister Abiy Ahmed Ali
Gwamnatin Habasha ba ta tsira daga sukar Bekele baHoto: Minasse Wondimu Hailu/AA/picture alliance

A shekara ta 2005 hukumomin Habasha sun kame Bekele, suka daure shi har tsawon shekara daya da rabi. Babban laifinsa a lokacin shi ne: Sukar tsarin zaben da aka yi kasar a wancan lokacin, da wasu ke zargin hukumomi sun nuna murdiya da aikata danniya. Bayan da aka sako shi, dan fafutukar ya zama darakta a kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, Human Rights Watch a Habasha a shekara ta 2011. Ya kuma hadu da abokan aikin da su kansu ke jinjina wa kwarewarsa.

Abokinsa Fikre Zewde ya rika kai wa lauyan ziyara a lokacin da yake a daure a gidan kaso. Ya ce "A lokacin da suka daure shi a gidan maza, hukumomi sun so durkusar da ayyukan 'yan fafutuka na shiga cikin mawuyacin hali kwarai. Sai dai shi Bakele ya nuna dattaku. Ina sha'awar wannan halayya tasa ta nuna dattaku."

Wannan dattakun ne har wa yau har magajin gobe, wadanda suka yi aiki tare da Daniel Bekele ke tunawa a duk lokacin da aka ambaci sunansa, duk kuwa da cewa a yanzu Habasha ta sake tsunduma cikin kogin take hakkin dan Adam a sakamakon rikicin da dakarun  gwamnati da na 'yan tawayen yankin Tigray na TPLF ke gwabzawa.

Me Bekele zai ce a kan rikicin Tigray?

Äthiopien Mekele | Pro-TPLF Rebellen
Rikicin yankin Tigray na ci wa Bekele tuwo a kwaryaHoto: YASUYOSHI CHIBA/AFP

A lokacin da yake tsokaci kan rikicin aware na yankin Tigraya Bekele ya ce ".Abin takaici, Habasha ta jima tana gadar rikicin siyasa mai sarkakiya wanda ya jefa kasar cikin tashin hankalin da ke bayar da damar take hakkin dan Adam cikin sauki. Wannan babu shakka ya haifar mana komabaya a aikinmu na kare hakkin dan Adam."

A farkon watan Nuwambar nan ne gwamnatin Habasha ta kafa dokar ta baci da zummar magance rikicin yankin Tigray da ke barazanar rugujewar gwamnatin kasar. Masu sharhi na zullumin cewa hukumomin za su yi amfani da sabuwar dokar wurin halasta cin zarafin dan Adam. Sai dai Daniel Bekele ya sha alwashin ci gaba da sanya ido a kan duk farar hula da gwamnati ta yi amfani da damar hakan ta keta wa rigar mutunci.

Kyautar da aka mika wa Daniel Bekele a ranar Alhamis (18.11.20219 da ake wa lakabi da  ''Deutscher Afrikapreis''  an fara ta tun a shekara ta 1993. Kuma wannan shi ne  karon farko da wani dan kasar Habasha ya taba samun ta.

Maria Gerth Maria Gerth