1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bazuwar murar tsuntsaye a Najeriya

February 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7M

Gwamnatin Najeriya ta bada tabbacin bazuwar cutar murar tsuntsaye zuwa wasu jihohin arewacin kasar 3 kuma,wanda a yanzu ya kawo yawan jihohi da cutar ta bulla zuwa jihohi 7 a Najeriyar.

Ministan yada labarai,Frank Nweke,ya fadawa manema labarai cewa ya zuwa yanzu dai jihohin Kano,Kaduna;Plateau,Bauchi,Katsina da Zamfara da kuma babban birnin taraiya Abuja an samu tabbacin isar kwayar cutar ta murar tsuntsaye.