Barazanar yunwa na karuwa a Najeriya | Labarai | DW | 17.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar yunwa na karuwa a Najeriya

Karancin kudade na iya jefa miliyoyin 'yan Najeriya cikin bala'in 'yunwa nan da makonni masu zuwa a cewar MDD. Wannan matsalar dai ta shafi yankin Arewa maso gabashin kasar da ke dauke da miliyoyin 'yan gudun hijira.

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce ga alamu miliyoyin 'yan Najeriyar za su fuskanci ja'ibar 'yunwa, lamarin da ya ce ka iya zama babbar matsalar jin kai a duniya. Wannan dai gargadi ne na yiwuwar samun karancin kudade daga Asusun samar da Abincin ga kimanin mutane miliyan 4 da dubu 700 da suka fuskanci matsalar tsaro na Boko Haram a kasar.

Wasu daga cikin mutanen da ke zama a sansanonin hijira ma sun tabbatar da karancin abincin. Bayanai na cewa kudaden da ke hannun masu samar da abincin ba za su wuce samar da abincin nan da ranar 18 ga watan gobe na Mayu ba.

A bayyane yake cewar yankin Arewa maso gabashin Najeriya na kan ganiyar iya fuskantar matsanancin karanci na abinci, sakamakon tsayar da harkokin noma da aka samu bayan da rigimar Boko Haram ta tsanata a yankin.